Shugaban Amurka Donald J Trump
Sakamakon wata ƙididdiga ya nuna cewa, tun bayan da aka kammala yaƙin duniya na biyu, har zuwa shekarar 2001, daga cikin tashe tashen hankula 248 da suka faru a yankuna 153 dake faɗin duniya, ƙasar Amurka ce ta tayar da 201, kuma yaƙe-yaƙe da ta tayar bisa fakewa da “yaƙi da ta’addanci”, tuni sun riga sun hallaka mutane sama da dubu 900 a cikin shekaru 20 da suka gabata.
