Mohammad Javad Zarif, tsohon ministan wajen Iran, ya gargaɗi Isra’ila da ta guji sake kai hare-hare kan Iran, yana cewa hakan ne mafi alheri gare ta.
A Taron Doha 2025, Zarif ya ce Isra’ila ta san Iran na da ƙarfi amma ba ta son faɗa sai don kare kanta. Ya bayyana cewa sabon harin da Isra’ila ta kai wa Iran kuskure ne wajen yin lissafi, wanda ya jawo yaƙin kwanaki 12 da ya kashe mutane sama da 1,064, ciki har da sojoji, masana nukiliya, da fararen hula.Amurka ma ta shiga rikicin ta hanyar kai hari kan wuraren nukiliyar Iran, abin da Iran ta kira take hakkin ƙasa da ƙasa.A ƙarshe, Iran ta mayar da martani ga Isra’ila da Amurka, lamarin da ya tilasta dakatar da hare-haren.
