Wasu ƙasashe da dama sun yi Allah-wadai da sanarwar shugaban Amurka Donald Trump na rufe sararin samaniyar Venezuela, suna kiran matakin “wanda ba bisa ka’ida ba aka gabatar da shi ba”, tare da gargaɗi game da illolinsa ga tsaron duniya, musamman a Latin Amurka da yankin Caribbean.
Iran ta yi tsattsauran suka ta bakin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ta, Ismail Baqaei, inda ya ce matakin da Trump ya ɗauka “mataki ne na son rai”. Ya ce:
“Wannan matakin na Amurka keta tsantseni ne ga doka ta kasa da kasa kuma barazana ce ga tsaron zirga-zirgar jiragen sama na duniya.”
Ya ƙara da cewa:” “Wannan shawara tana cikin jerin matakai masu tayar da hankali waɗanda ke keta ikon Venezuela da kariyar iyakokinta.”
Ya ci gaba da gargaɗi yana mai cewa:” mummunan tasirin da wannan mataki zai haifar ga mulkin doka da zaman lafiya da tsaron duniya.”
A nasa ɓangaren, shugaban Kolombiya Gustavo Petro, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar ƙasashen Latin Amurka da Caribbean, ya yi Allah-wadai da sanarwar Trump, yana mai cewa:“Rufe sararin samaniyar Venezuela ba bisa ƙa’ida ba ne.”
Ya kuma kira ICAO (Ƙungiyar Kasa da ƙasa ta Harkokin Jiragen Sama) da ta gaggauta taro don yin tir da shi.
A jawabin da ya yi ranar Lahadi 30 ga Nuwamba 2025, Petro ya ce: “Ba a ba da izinin Majalisar Tsaro ko Majalisar Dokokin Amurka don ɗaukar matakan soja kan Venezuela.”
A wani rubutu da ya wallafa a X jiya Asabar, Petro ya ce:“Ba za a yarda wani shugaban ƙasa na waje ya rufe sararin samaniyar wata ƙasa ba. Idan hakan ta faru, to ikon ƙasa da doka ta duniya sun mutu.”
Ministan harkokin wajen Cuba, Bruno Rodríguez Parrilla, shi ma ya yi Allah-wadai da matakin, yana kiran shi: “Aiki na tashin hankali da barazana mai tsanani ga doka ta ƙasa da ƙasa.”
A rubutunsa a X, ya ce: “Wannan mataki barazana ce mai tsanani ga doka ta duniya, yana kuma kara hura wutar tashin hankalin soja da yaƙin tunani kan al’ummar Venezuela, da tasirin da ba za a iya hango iyakarsa ba ga zaman lafiya da tsaro a Latin Amurka da Caribbean.”
Ya roƙi al’umma ta duniya da ta: “yi tir da matakin da ke shirin kai hari ba bisa ka’ida ba.”
Shugaba Trump ya sanar a Truth Social jiya Asabar cewa:“Ya kamata a ɗauki sararin samaniyar Venezuela a rufe gaba ɗaya.”
Wannan na faruwa ne yayin da Amurka ke ƙarawa matsa lamba na soja kan Caracas ta hanyar aika manyan jiragen yaki, jiragen ruwa masu dauke da makamai, da sojoji zuwa yankin Caribbean.
A nata bangaren, Venezuela ta zargi Trump da: “barazanar mulkin mallaka.”
Ma’aikatar harkokin wajen Venezuela ta bayyana kalaman Trump da: “tayin harin da bai dace ba, ba bisa ƙa’ida ba, kuma ba shi da tushe a kan jama’ar Venezuela.”
Sanarwar Trump ta zo ne bayan da hukumomin zirga-zirgar jiragen sama na Amurka suka gargaɗi jiragen fararen hula da ke shawagi a sararin samaniyar Venezuela da su:“yi taka tsantsan saboda tabarbarewar tsaro da karuwar ayyukan soja a Venezuela da kewaye da ita.”
