Rundunar Sojojin Najeriya a Zariya, Jihar Kaduna, Najeriya ta kai hari kan Musulmi ‘yan Shi’a, galibi ‘yan Harkar Musulunci a Najeriya, a ranar 12 ga Disamba, 2015.
Harin ya yi sanadin salwantar rayukan daren fararen hula dubu ɗaya waɗanda akwai sunayensu da sosai garuruwan da suka fito. Harin wanda ya kai ga jiwa adadi masu yawa miyagun raunuka waɗanda wasu har yanzu ba su warke ba.
Bayan ƙaddamar da kisan kiyashin Gwamnatin Jihar Kaduna ta bizne jikin waɗanda aka kashe a ƙabarin bai-ɗaya a Mando Kaduna.
Rundunar sojin ta yi iƙirarin cewa ta mayar da martani ne kan yunkurin kashe shugaban hafsan sojin Najeriya Janar Tukur Buratai da kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya ta yi.
Wannan iƙirari dai ya sha kakkausar suka daga Harkar Musulunci da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da dama waɗanda ke ganin cewa kisan kiyashin ya faru ne ba tare da wani tayar da hankali ba, kuma duk waɗanda aka kashe ba sa dauke da makamai. Ana ɗaukar lamarin a cikin “sanannen take haƙƙin ɗan adam tun dawowar dimokuradiyya” a Najeriya.
Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zenarudeen Ibraheem Allah ya tseratar da su da miyagun raunukan da ya kuɓutarsu ya zamanto wani lamari na abun mamaki a rayuwar ɗan Adam
An ƙona wasu gawarwakin waɗanda suka jikkata da ransu, a cewar rahoton Amnesty International.
A cewar rahoton na HRW, gwamnatin Najeriya ta binne gawarwakin ba tare da izinin ‘yan uwa ba.
A ranar 22 ga Afrilu, 2016, ƙungiyar Amnesty International ta buga shaidun da aka tattara na gani da Ido da ke nuna yadda sojojin Najeriya suka ƙona mutane da ransu, da ƙona gine-gine da Miliyoyin kuɗaɗe, haɗe da zuwa Darur Rahama da ke ƙauyen Dambo Zariya in da suka tone ƙabarurrukan ‘ya’yan Harkar Musulunci.
Hakama ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya, Human Rights Watch, ta ce sojojin Najeriya ba su da wata hujjar kashe ‘yan Shi’a a Zaria, duk da iƙirarin da suka yi cewa mabiya Shi’ar sun yi yunƙurin kashe Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai. Human Rights Watch ta ce , “Mun tattauna da shaidu 16 da kuma wasu biyar — cikinsu har da shugabanni — waɗanda suka gaya mana cewa sojojin Najeriya sun yi ta harbin kan mai-uwa-da-wabi a cibiyoyi uku na ‘yan Shi’a a Zaria daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Disamba.
Ba zai yiwu a ce tare hanyar da ‘yan ƙungiyar suka yi ya zama hujjar kashe daruruwan mutane ba”.
Ƙungiyar ta kara da cewa, “Sojoji sun kai hare-hare kan cibiyar Hussainniya Baƙiyyatullah, da gidan shugaban ‘yan Shi’a, Sheikh Ibrahim Al Zakzaky da gidajen maƙwabtansa da ke Gyellesu da kuma makabartar ‘yan Shi’a, Daral-Rahma, a cikin kwanaki biyu.
Bincike
A watan Janairun 2016 ne gwamnatin jihar Kaduna ta kafa kwamitin bincike na shari’a kan musabbabin tashin hankalin na watan Disambar 2015, karkashin jagorancin Mai shari’a Mohammed Garba, alƙalin kotun Fatakwal sashen Kotun Daukaka Kara.
Sakamakon bincike
A ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2016, kwamitin bincike ya gano cewa sojojin kasar sun bindige mabiya mazhabar Shi’a 348 tare da neman a hukunta duk waɗanda ke da hannu a kisan.
Farar takarda da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar kan rahoton ta yi watsi da yawancin shawarwarin da hukumar ta bayar.
Bayan shekaru 10, babu wani soja ko jami’in soji da aka ɗora wa alhakin kashe-kashen, wanda ya kai ga zargin wani na rashin hukunta su. Ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama kamar Amnesty International da Human Rights Watch na ci gaba da yin kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa tare da yin adalci ga iyalan wadanda abin ya shafa.
Iyalan waɗanda suka tsira da wadanda abin ya shafa har yanzu suna fama da tsananin baƙin ciki da raunin rashin ‘yan uwa da rashin yi musu jana’izar da ta dace.
Kisan gillar da aka yi a Zariya ya kasance wani muhimmin batu da ba a warware shi ba a Najeriya, inda ake ci gaba da kiraye-kirayen ɗaukar matakin yin adalci.
Jiga-jigan waɗanda suka jiƙa hannayensu da jine-nan ‘yan uwa Musulmi sun haɗa da Marigayi Muhammad Buhari, tsohon hafsan Hafsoshin Nijeriya Tukur Y.Buratai, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmed Elrufa’i waɗanda Buhari ne kaɗai ya mutu a cikin ukun nan, amma biyu ɗin na nan suna ci gaba da shaƙar iskar ‘yancin rayuwa ba tare da an hukunta su ba.
