Mahaifiya da ɗan ta da harin HKI ya kashe
An samu rahoton cewa jaririn Fâlasɗinu, Osama Abu Snineh, da mahaifiyarsa sun rasa rayukansu a sakamakon hare-haren jiragen sama na haramtacciyar Kasar Izrâilâ a zirin Gãzâ.Lamarin na Osama Abu Snineh yana ɗaya daga cikin munanan misalai na asarar rayukan fararen hula da suka faru a yankin. Hare-haren sama sun ci gaba da haifar da mummunan bala’i ga iyalai a Gãzâ, inda suka yi sanadiyyar mutuwar yara ƙanana da kuma share iyalai gaba daya daga rayuwa.— Shamsudeen Adamu Alshirazy| ABS Radio.30/10/2025
