Daga Shamsudeen Adamu AlshirazyABS Radio — 31 Oktoba, 2025
Kowane shekara idan watan Oktoba ya zagayo, zukata kan yi rawar jiki, idanun masu imani sukan cika da hawaye, wajen tunawa da abin bakin ciki na Kisan Kiyashin Abuja na 2018, lamarin da ya kai ga zubar jinin ma su imani da gaskiya a titunan babban birnin Najeriya, Abuja.
A waccan shekara ta 2018, a ranakun 27, 29 da 30 ga Oktoba, rundunar sojojin Najeriya ta yi wa mabiya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wadanda suke yin Arba’een ta tunawa da shahadar Imam Husain (A.S), kisan kiyashi yayin da suke tafiyar su na tattaki.Tafiyar Arba’een hanya ce ta soyayya, hakuri da tunawa, ana yin ta domin girmama sadaukarwar Imam Husain (A.S), jikan Manzon Allah (S.A.W), wanda ya tsaya ga gaskiya da adalci a filin Karbala.
Amma a shekara ta 2018, yayin da muminai ke tafiya cikin salama suna tuna wannan al’amari na Imam Husain(AS), su ma suka gamu da irin zaluncin Karbala ta zamani, ba a cikin hamadar Iraki ba, sai dai a cikin titunan Abuja.Lamarin ya fara ne a ranar 27 ga Oktoba, a gadar Zuba-Abuja, inda karar harbi ta fara kamar tsawa. Mutane marasa makamai mata da maza dauke da tutoci da alamomin Imam Husain (A.S), suka hadu da harsasai.
Sojoji suka bude wuta ba tare da jin tausayin rai ba. Manya da ƙanana suka faɗi, uwa ta kira ɗanta, ɗan’uwa ya kira ɗan’uwa, suka zama shahidai akan tafiyar imani.Ranar 29 ga Oktoba, an sake zub da jini a gadar Karu, kusa da wani shingen soja a wani yanki na jihar Nasarawa.
Sojoji sun sake bude wuta kan masu tafiya cikin lumana. Shaidu sun bayyana yadda ake harbi ba kakkautawa, kamar dai ana yakin abokan gaba. Amma duk da haka, bakin masu tafiyar tattakin bai daina cewa “Labbaika Ya Husain!” — “Ga mu nan, Ya Husain!”Sai ranar 30 ga Oktoba, 2018, lamarin ya kai kololuwa a Central Area na Abuja, kusa da Ofishin Kare Hakkokin Dan Adam na Kasa (NHRC). A nan ma, an sake bude wuta. Gaban ginin gwamnati, tituna suka sake yin ja, mutane da dama suka rasa rayukansu, wasu da yawa suka ji rauni, wasu kuma aka kama aka dauke su.
A cikin kwana uku, babban birnin kasar ya zama shaida ga kisan kiyashi ba na ‘yan ta’adda ba, sai dai na ‘yan kasa masu neman adalci da tunawa da gaskiya.Kungiyoyin kare hakkin dan Adam kamar Amnesty International sun yi Allah wadai da wannan kisa, suna cewa ya sabawa duk wata ka’idar jin kai da dokokin duniya. Amma har yau, shekaru bakwai bayan faruwar lamarin, babu wanda aka hukunta. Jinin marasa laifin da aka zubar yana cigaba da kiran adalci daga ƙasa.
Yau, yayin da muke tunawa da shahidai 50 wanda aka raba su da wannan duniyar, ba kawai rashin su muke tunawa ba, har da imanin su mai ƙarfi. Sun yi bar duniya da ruhin Imam Husain (A.S), aka kashe su kamar shi, ana zaluntar su, amma su ne da nasara.
Domin kowanne digo na jinin su tsiro yake a zukatan masu gaskiya, yana furta cewa “Gaskiya ba ta mutuwa da harsashi.”Kisan Kiyashin Abuja na 2018 ya kasance tabo a ran ƴan kasa ma su kishin adalci, tunatarwa ce cewa hanyar adalci tana da tsayi, amma muryar gaskiya ba ta taɓa mutuwa ba.
#AbujaMassacre#7YearsAbujaMassacre
