Shugaban Amurka Donald J Trump
*Cikin Shekaru 250, Amurka ta Mamaye Tare da Yakan Kasashe 43, Bisa Zalunci, Ta Kuma Kifar Da Gwamnatocin Kasashe….* Daga Yusuf KabiruDuk da cewa ba a wuce shekaru kusan 250 da ƙirƙirar Amurka, an samu ta ta shafe 93% na tarihin ta — wato kusan shekaru 222 — tana cikin yaƙe-yaƙe daban-daban da mamayar ƙasashe a duniya. Fiye da yaƙe-yaƙe 90, mafi yawansu laifukan yaƙi, suna nuna cewa ita ce ɗaya daga cikin ƙasashe mafi zalunci da munafurci da ta taɓa wanzuwa a tarihin ɗan Adam. Ga jerin wannan “jerin baki” kamar haka:1. 1833 — Sojojin Amurka sun mamaye Nikaraguwa.2. 1888 — Sojojin Amurka sun shiga Peru.3. 1846 — Sun mamaye ƙasar Mexico, suka haɗa ta da ƙasar su (yanzu Texas).4. 1848 — Sun ƙara mamaye wasu yankuna na Mexico (yanzu California da New Mexico).5. 1854 — Sun lalata tashar jiragen ruwa ta Grey Town a Nikaraguwa.6. 1855 — Sun kai hari kan Uruguay da Panama.7. 1857 — Sun sake shiga Nikaraguwa don hana ɗan adawa da su, William Walker, hawa mulki.8. 1873 zuwa 1899 — Mamaye da hare-hare kan Kolombiya.9. 1888 — Tsoma baki a Haiti.10. 1891 — Tsoma baki a Chile.11. 1894 — Sake tsoma baki a Nikaraguwa.12. 1898 — Mamaye Cuba da kwace Guantánamo Bay.13. 1901-1902 — Tsoma baki a Kolombiya.14. 1902 — Tsoma baki a Honduras.15. 1904 — Hari kan Panama.16. 1905 — Hari kan Honduras.17. 1907 — Sun mamaye garuruwa shida a Honduras.18. 1907 — Hari kan Mexico don taimaka wa mai mulki Porfirio Díaz.19. 1907 — Hari kan Nikaraguwa.20. 1907 — Mamaye Dominican Republic.21. 1908 — Shiga yaƙin Honduras da Nikaraguwa.22. 1910 — Tsoma baki a zaɓen Panama.23. 1911 — Tsoma baki a Nikaraguwa.24. 1911 — Tsoma baki a Honduras don tallafa wa juyin mulki.25. 1911 — Murkushe tawayen Philippines.26. 1912 — Tsoma baki a China.27-29. 1912 — Hare-hare a Cuba, Panama, da Honduras.27. 1914 — Sojojin Marines sun shiga Haiti, suka kwashe kuɗin bankinta.28. 1915-1934 — Mamayar Haiti gaba ɗaya.29. 1916-1924 — Mamayar Dominican Republic.30. 1917 — Mamayar Cuba.31. 1918 — Shiga Yaƙin Duniya na Ɗaya.32. 1918-1920 — Tsoma baki a Rasha.36-39. 1919-1921 — Hare-hare a Panama, Costa Rica, Honduras, Guatemala.33. 1922 — Tsoma baki a Turkiyya da El Salvador.42-47. 1924-1933 — Hare-hare masu yawa a China, Honduras, Panama, Nikaraguwa.34. 1934 — Mamayar Haiti.35. 1937 — Hari kan El Salvador.50-51. 1945 — Bama-baman nukiliya a Hiroshima da Nagasaki (mutane ~220,000 sun mutu).52-55. 1947-1950 — Tsoma baki a Girka, Filipin, Puerto Rico, da Koriya.36. 1953 — Juyin mulkin Iran, da kifar da Mohammad Mossadegh.37. 1954 — Hambarar da gwamnati a Guatemala.58-61. 1958-1959 — Hare-hare a Koriya, Lebanon, Panama, Laos.62-63. 1960 — Hare-hare a Haiti da Ecuador.64-65. 1961-1962 — Mamayar Bay of Pigs da Cuban Missile Crisis.66-67. 1965-1975 — Yaƙin Vietnam, inda aka yi manyan laifukan yaƙi da amfani da sinadarai.68-74. 1966-1973 — Hare-hare a Guatemala, Cambodia, Laos, da juyin mulki a Chile.75-83. 1980-1989 — Tsoma baki a Nikaraguwa, Grenada, Libya, Panama, da Iran.84-85. 1991 — Yaƙin Gulf da Iraq.86-88. 1995-1998 — Bosnia, Somalia, da Sudan.38. 2001 — Yaƙin Yugoslavia (ta hanyar NATO).39. 2001 — Mamayar Afghanistan.40. 2003 — Mamayar Iraq.41. 2011 — Hari kan Libya.42. 2011 — Tallafa wa ’yan ta’adda a Syria.43. 2015 — Hari kai tsaye kan Yemen da makaman da aka hana amfani da su.A takaice, wannan tarihin yana nuna yadda Amurka ta yi amfani da ƙarfin soja wajen mamaye ƙasashe da tsoma baki cikin harkokin su, tun daga ƙarni na 19 har zuwa ƙarni na 21.
