Daga Yusuf Kabir Roni
Kwamitin Amintattu na Jami’ar Tazkiyah, Kaduna, ya amince da naɗin Farfesa (Hajiya) Bilkisu Aminu Shinkafi daga sashen Zoology na Jami’ar Abuja, a matsayin Mataimakiyar Shugabar Jami’a (Vice Chancellor) ta farko ta jami’ar, na tsawon shekaru biyar, daga yanzu.
Farfesa Shinkafi kwararriya ce kuma gogaggiyar malama da ta shafe fiye da shekaru ashirin tana koyarwa, bincike, da gudanar da harkokin jami’a. Ta taɓa riƙe mukaman Mataimakiyar Shugabar Jami’a (Academic), da riƙe shugabar tsangayar Kimiyya, sannan ta zamanto mamba a Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Tarayya, Gusau, da sauran manyan muƙamai da ta riƙe.
A halin yanzu, Farfesa Shinkafi wakiliyar shugaban ƙasa ce a Majalisar Gudanarwa ta Kwalejin Ilimi ta Fasaha (Federal College of Education Technical), Gusau.
Malamar mai jajircewa ce a fannin ilimi, wacce ke da hannu a gudanarwar ƙungiyoyi da dama na masana kimiyya, ciki har da Science Association of Nigeria, Fisheries Society of Nigeria, da Association of African Universities.
Al’ummar Jami’ar Tazkiyah ta taya Farfesa Shinkafi murna bisa wannan naɗin, tare da fatan Allah ya mata jagora kuma ya bata nasara a zangon Shugabancin da za ta yi.
