Ƙasar Saudiyya ta ƙara zuba hannun jari a Amurka daga dala biliyan 600 zuwa kusan dala tiriliyan 1, in ji Anadolu.
“Ina ganin, Shugaba, a yau da gobe za mu iya sanar da cewa za mu ƙara waɗannan dala biliyan 600 zuwa kusan dala tiriliyan 1 na sahihin jarin da za a zuba,” in ji Bin Salman, wanda aka fi sani da MBS, yayin da yake magana da ’yan jarida a Fadar White House tare da Shugaban Amurka Donald Trump.
Ya ce ƙasashen biyu za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama a fannoni iri-iri, ciki har da fasaha, basirar wucin-gadi (AI) da na’urorin maganaɗisu, “waɗanda za su samar da dama mai yawa ta zuba jari.”
A yayin da Muhammad bn Salman yake ci gaba da bayani a fadar White House, sai Trump ya katse shi, yana cewa: “Yanzu kana gaya mini cewa waɗannan dala biliyan 600 za su zama dala tiriliyan 1?”
“Tabbas, saboda abin da muke rattabawa zai ba da damar hakan,” in ji Bin Salman.
Trump ya yi masa godiya saboda amincewa da zuba jarin.
“Ina so in gode maka saboda ka amince ka zuba dala biliyan 600 a Amurka, kuma saboda abokina ne, wataƙila zai mai da shi tiriliyan 1, amma zan ci gaba da lallaɓarsa,” in ji shi.
“Za mu iya dogaro da dala biliyan 600, amma wannan adadi na iya ƙaruwa kaɗan,” in ji Trump, cikin salon sa na nuna irin abin da hulɗarsa da ƙasashen waje ke samarwa ga Amurka.
Jakadiyar Saudiyya a Amurka, Princess Reema Bint Bandar Al-Saud, ta yabawa ganawar da ta gudana tsakanin MBS da Trump bayan rattaba hannu kan wasu manyan yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashen biyu.
“Wata rana mai muhimmanci ga dangantakar Saudiyya da Amurka,” in ji jakadiyar a dandalin sada zumunta na X.
Ta ce ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan “jerin muhimman yarjejeniyoyi” na ɓangarorin biyu, ba tare da bayyana cikakkun bayanai ba.
“Waɗannan yarjejeniyoyi za su ƙarfafa saka hannun jari a ƙasashen biyu, su samar da damar aiki ga ’yan Saudiyya da ’yan Amurka, kuma su inganta jajirtattun alƙawurranmu na tsaron yankin da na duniya,” ta ƙara da cewa.
