Hukumar Tsaro ta DSS ta shigar da ƙarar aikata ta’addanci a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan wasu manyan kwamandojin IPOB guda bakwai da ake dangantawa da Simon Ekpa.
A cikin shari’o’i uku dabam-dabam — FHC/ABJ/CR/632/2025;
FHC/ABJ/CR/633/2025;
FHC/ABJ/CR/634/2025 da aka shigar a ranar 19 ga Nuwamba, ana zargin waɗannan mutane da karɓar kuɗi da kayan tallafi daga Simon Ekpa da wasu ’yan IPOB da ke ƙetare.
Wani muhimmin mutum da ake zargi, Ibrahim Ali Larabo, wanda ake zargin ya riƙa ba da kuɗaɗen tallafa wa ta’addanci, ba dan Najeriya ba ne; baƙauyen ɗan ƙasar Nijar ne kuma yana gudanar da Bureau de Change (BDC) ba tare da lasisi ba. Ya riƙa ba da hidimar kuɗi ga ƙungiyar IPOB ta Simon Ekpa, yana karɓa kuma yana rabon manyan kuɗaɗe don ayyukan ta’addanci a yankin Kudu maso Gabas.
An tabbatar cewa waɗanda ake tuhumar su komandoji ne na IPOB, ’yan safarar makamai, mayakan ESN da kuma masu aikata hare-hare, waɗanda Simon Ekpa — wanda aka riga aka yanke wa hukuncin shekara shida a Finland kan laifukan ta’addanci — ke bai wa umarni da kuɗaɗe.
A wata sanarwa da Favour Dozie, Mataimakin Darakta na Sashen Hulda da Jama’a da Tsare-Tsaren Yaɗa Labarai na DSS ya fitar, hukumar ta bayar da karin bayani kan sauran shari’o’in da ta gurfanar da wasu ’yan ta’adda:
DSS ta gurfanar da Ismaila (mai suna Mai Tangaran), ɗan ta’addan da ya kitsa harin 2012 a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Kano, da sauran wuraren gwamnati. An same shi da laifi a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Shari’ar ta fara tun 2017, ta kuma ƙare a ranar 18 ga Nuwamba da hukuncin kotu.
Ismaila, wanda ɗaya ne daga cikin shugabannin ISWAP, an same shi da laifi kan tuhuma huɗu da DSS ta shigar ƙarƙashin Dokar Karewa Daga Ta’addanci (gyararraki) ta 2013. Mai shari’a Nwite ya yanke masa shekara 15 kan tuhuma ta farko, sannan shekara 20–20–20 kan sauran tuhumomin uku, duk su gudana lokaci guda.
DSS ta riga ta shigar da ƙara kan wasu fitattun ’yan ta’adda biyu da ake nema a ƙasashen waje ,Mahmud Muhammad Usman (Mamuda) da Abubakar Abba (Abu Baara) — shari’arsu za ta ci gaba a gaban Mai Shari’a Nwite a ranar 15 Janairu 2026.
Haka kuma ana ci gaba da shari’ar Khalid Al-Barnawi, wanda ake zargin jagoran harin gine-ginen Majalisar Dinkin Duniya da aka kai a 26 Agusta 2011 a Abuja. Shi da wasu huɗu suna fuskantar tuhumar harin.
Wasu mutane biyar kuma an gurfanar da su kan tuhuma tara (9) a Babbar Kotun Tarayya Abuja (shari’a mai lamba FHC/ABJ/CR/301/2025) kan rawar da suka taka a harin da aka kai Cocin Katolika St. Francis, Owo, ranar 5 ga Yuni 2022.
DSS tana shari’a kan wasu mutum goma da ta kama a Benue da Filato bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na kama duk masu hannu a hare-haren yankunan.
Haka zalika, za a gurfanar da Abdulazeez Obadaki (Bomboy), wata sanannen jagoran ISWAP da aka sake cafke shi, wanda ya amsa laifin kitsa harin Cocin St Francis, Owo da Cocin Deeper Life, Okene; da kuma Musa Abubakar, babban mai kera da rarraba makamai da aka kama a Filato.
Daraktan DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi, tun bayan hauhuwar sa kan kujerar shugabanci a Agusta 2024, ya ba da umarnin duba dukkan shari’o’in da ya gada tare da aiwatar da binciken kwararru (forensics) domin tabbatar da gurfanar da ’yan ta’adda yadda doka ta tanada.
