Biyo bayan barazanar da Donald Trump ya yi cewa zai tura sojoji Amurka zuwa Najeriya, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta mayar da martani
A ranar Lahadi, tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar tura rundunar sojojin Amurka zuwa ƙasar Nigeria don yakar ‘yan ta’addan musulmi daban-daban da ya ke ikirarin suna kashe Kiristoci a Najeriyar.
Trump ya ce, idan gwamnatin Tinubu ba ta ɗauki matakin dakile irin wannan kashe-kashen ba, Amurka za ta dakatar da duk tallafin da take ba Najeriya, kuma “za mu shiga”, kamar yadda ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa.
Amma gwamnatin Shugaba Tinubu ta mayar da martani tana ƙaryata abin da Trump ya ce — ta ce Najeriya na da tsarin doka da ya tabbatar da ‘yancin addini,
