Rahotannin dake shigo mana a halin yanzu sun tabbatar mana da mutuwar ƙasurgumin Ɗan bindigar nan mai suna Jan Kare.
Ƙasurgumin Ɗan bindigar ya gamu da ajalin sane da hantsin ranar Alhamis din nan 30/10/2025.
Tubabben Ɗan bindigar nan na yankin Safana da ya rungumi zaman lafiya bayan sasancin da akayi a yankin Safana, Kurfi da Dutsinma watau Sani Mohindinge ya yi ajalin na Jan Kare.
Bayan samunsa da laifin tare wasu mutane ya amsar masu kudi dubu talatin da kuma wayoyin hannusu, bayan kuma anyi sasanci tare da yarjejeniyar zaman lafiya a yankin na Safana, Kurfi da Dutsinma.
Kasurgumin Ɗan bindigar Jan Kare yana cikin wanda su ka hadu da su Sani Mohindinge da sauran yan bindigar su ka amince da sulhun yarjejeniyar zaman lafiya a yankin Safana, Kurfi da Dutsinma.
Hoto na farko daga cikin waɗannan hotunan dake kasa shine Sani Mohindinge da ya kashe Kasurgumin Ɗan bindiga Jan Kare.
Hoto na biyu kuma shine Kasurgumin Ɗan bindigar Jan Kare, Mobile Media Crew ta ɗauke su hoton a taron sulhun zaman lafiya da akayi na ƙaramar Kurfi ta Jihar Katsina.
