Daraktan Janar na Ofishin Yaɗa Labaran Gwamnati a Gaza, Dokta Isma’il al-Thawabta, ya yi gargaɗi game da wani mummunan bala’i ke tunkaro al’ummar Palasɗinu a yayin da lokacin sanyi ke ƙaratowa. ,Hakan sakamakon haramtacciyar ƙasar Isra’ila ke ci gaba da hana shigar da tantuna, tabarma, da iskar gas ɗin girki zuwa Zirin Gaza, duk da ɓarnar da ta shafi gidajen fararen hula da cibiyoyin ba da mafaka da suke ta ta yi a shekaru biyu na kisan kiyashin da suke a ZirinA cikin wata sanarwa da Cibiyar Yaɗa Labaran Falasɗinu ta ruwaito, al-Thawabta ya bayyana cewa, wannan haramcin ya ƙara tsananta halin da fiye da mutum miliyan ɗaya da rabi ke ciki — waɗanda ke zaune a fili ko cikin tsofaffin tantuna waɗanda ba sa kare su daga sanyi ko ruwan sama idan an yi. Ya jaddada cewa hana kayan da za a samar da Tantuna, man fetur, da iskar gas ɗin girki babban laifi ne da ke tauye haƙƙin ɗan adam, kuma ya saɓa da dokokin ƙasa da ƙasa da yarjejeniyoyin Geneva, waɗanda ke wajabta wa ƙasar mamaya ta samar da buƙatun rayuwa ga fararen hular na Gaza.Ya ƙara da cewa, waɗannan matakai suna cikin manufar hukuncin haɗin gwiwa (collective punishment) da Isra’ila ke amfani da ita kan al’ummar Gaza, yana bayyana hakan a matsayin ci gaba da “yaƙin yunwa, ƙauracewa, da halakar da rayuka a hankali” da ake yi wa mutanen Falasɗinu tun lokacin da yaƙin ya fara.A wani ɓangare, al-Thawabta ya bayyana ƙoƙarin da Ma’aikatar Ilimi da ma’aikatan cibiyoyin ilimi ke yi domin farfaɗo da tsarin karatu duk da barnar da aka yi. Ya bayyana cewa makarantu da jami’o’i da dama sun lalace gaba ɗaya ko a wani ɓangare, abin da ya hana ɗalibai kusan 800,000 damar karatun su na yau da kullum.Duk da haka, ya ce tsananin wahala bai hana malamai da al’umma ƙaddamar da shirye-shiryen ilimi na gaggawa ba, ta hanyar buɗe ajujuwa a cibiyoyin ba da mafaka da sauran wuraren da suka dace, don samar da yanayin karatu mai aminci gwargwadon iko.Daraktan ya jaddada cewa Isra’ila ce ke da alhakin kan hana shigar da kayan agaji, musamman tantuna, kayan mafaka, iskar gas ɗin girki, man fetur, kayan karatu, da kayan koyarwa a makarantu.Al-Thawabta ya kira Majalisar Dinkin Duniya, ƙungiyoyin duniya, CICR (Ƙungiyar Jan Red Cross ta Duniya), UNDP, da ƙasashen Larabawa da Musulmi da su tashi tsaye su matsa lamba ga Isra’ila ta daina take-taken ta, tare da ba da damar shigar da duk kayan agaji ba tare da wani sharaɗi ba.A ƙarshe, ya jaddada cewa al’ummar Falasɗinu za su ci gaba da riƙe haƙƙin su na rayuwa cikin mutunci duk da yaƙi da takura, kuma za su ci gaba da gina ƙasa da farfaɗo da fannin ilimi, aiki, da mafaka. Ya ƙara da cewa:> “Lokaci ya yi da al’ummar duniya za ta ɗauki nauyin ta wajen dakatar da wannan laifi da ake yi a gaban idonta.”Isra’ila na ci gaba da kulle GazaOfishin Yaɗa Labaran Gwamnati ya bayyana cewa jimillar taimakon da ya shiga Zirin Gaza tun bayan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta bai wuce kashi 28% na abin da aka tsara ba.A cikin sanarwarsa ta ranar Alhamis, ofishin ya ce jiragen ƙasa 4,453 ne kawai suka shiga daga cikin jirage 15,600 da ya kamata su shiga zuwa daren Laraba. Wannan ya haɗa da motoci 31 masu ɗauke da iskar gas ɗin girki da motoci 84 masu ɗauke da man dizal don gudanar da masu gasa burodi, asibitoci, injuna, da sauran cibiyoyin muhimmanci — duk da ƙarancin wadannan kayayyaki da ake fama da shi bayan shekaru biyu na kisa, kulle, da lalata kai tsaye da Isra’ila ta yi wa Gaza.Sanarwar ta ƙara da cewa adadin motocin agaji da ke shiga kullum bai wuce 171 ba, daga cikin motoci 600 da aka tsara su rika shiga a kullum bisa tsarin agajin ɗan Adam. Wannan, in ji su, hujja ce cewa Isra’ila har yanzu na ci gaba da manufar takura, yunwa, da matsin lamba ga mutane 2.4 miliyan da ke Gaza.Har ila yau, sanarwar ta jaddada cewa waɗannan adadi ƙanana ne da ba su cika ma’aunin abinci, magani, da kayan rayuwa ba, kuma ana bukatar aƙalla motoci 600 a kowace rana da ke ɗauke da abinci, magunguna, man fetur, iskar gas ɗin girki, da kayan lafiya don tabbatar da ɗorewar rayuwa ta asali a Gaza.Majalisar Dinkin Duniya ta kira da a ƙara taimakon mafakaMajalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta da faɗaɗa shigar da kayan mafaka zuwa Gaza kafin lokacin sanyi, duba da yadda yanayin jin kai ke tabarbarewa da kuma ci gaba da takunkumin Isra’ila kan agajin.Farhan Haq, mataimakin kakakin sakataren janar na MDD, ya bayyana a wata tattaunawa da manema labarai cewa kungiyoyin agaji da ke aiki a Gaza suna ƙara ƙoƙarinsu a yankunan da a da suka kasance masu wuya a isa gare su.
