TONON SILILI; YADDA SAUDIYYA, (UAE), ƘATAR SUKA ƊAUKI NAUYIN YAƘIN DA ISRA’ILA TA ƘADDAMAR DOMIN RUSA GWAMNATIN IRAN
Daga Haj Emaad
Kafar yaɗa labaran WikiLeaks ta fallasa wanda ke daukar nauyin harin da Isra’ila ta kai kan a watannin baya kan kasar Iran.
A cikin wani sabon bincike mai haɗari da shafin WikiLeaks ya wallafa, an fallasa ɗaya daga cikin manyan makirce-makirce mafi muni a tarihin Gabas ta Tsakiya na zamani:
Yaƙi ne da Isra’ila ke gudanarwa, amma da kuɗin kasashen Gulf, domin rusa Hukumar Iran wacce ta zamanto babbar barazana ga Amurka da Isra’ila a gabas ta tsakiya.
Bayanan sun bayyana cewa, an fara shirya wannan lamari a asirce tun watanni da suka gabata A cewar takardun da aka fitar, shirin wannan yaƙin ya fara watanni da suka shige, a tarurrukan sirri da suka haɗa wakilan Isra’ila da Amurka da kuma jami’ai daga Saudiyya, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), da Qatar.
An cimma yarjejeniya mai cewa:
“Isra’ila za ta kai farmaki, ƙasashen Gulf kuma su bayar da maƙuden kuɗaɗen aiwatar da hakan.
Wani sashen rahoton ya bayyana cewa, an ƙayyade adadin kuɗin da za a kashe: dala tiriliyan ɗaya a matsayin farashin farko don “kawar da tsarin mulkin Iran.”
Takardun sun tabbatar da cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya taka muhimmiyar rawa a wannan yarjejeniya, inda ya ziyarci wasu manyan biranen Gulf a hukumance cikin ‘yan watanni da suka gabata, inda ya karɓi kuɗin da ake buƙata.
An ba shi adadin da aka nema, tare da ƙarin kashi 400%, domin ya tayar da rikici, ya kifar da gwamnatin Iran, kuma ya shiga cikin cibiyoyin tsaron ƙasar. Al’umma da dama sun yi zaton waɗannan ziyarce-ziyarce na Trump sun shafi zuba hannun jarin kasuwanci da dangantakar siyasa tsakaninsa White House da ƙasashen, sai dai lamarin ba haka yake ba.
A cikin watanni da suka wuce, kamfanonin makamai na Amurka da Turai sun ƙulla yarjejeniyoyi da Isra’ila a ɓoye, inda aka ba ya manyan makamai masu yawa – ciki har da miyagun bama-bamai, makaman roka masu nisa, da jiragen yaƙi marassa matuki (drones).
Duk wannan an shirya shi a ɓoye kafin Isra’ila ta za ta fara kai harin.
Ba Iran kaɗai ake nufi ba…
BA IRAN KAƊAI AKE NUFI BA
Abin da waɗannan takardu suka fallasa bai tsaya kan Iran kawai ba, lamarin ya tona asirin makircin wasu ƙasashen Larabawa da ke yaƙi da duk wanda yake goyon bayan Falasɗinu, da wanda yake tallafawa gwagwarmaya, wanda ya ƙi amincewa da “yarjejeniyar ƙarni” (Deal of the Century).
Kowacce roka da Isra’ila ke harbawa a kan Iran, ana biyan farashinsa da kuɗin man fetur da iskar gas na kasashen Gulf.
