Daga Zainab Ahmad
Jamhuriyyar Musulunci ta Iran ta sanar da cewa, nan gaba kaɗan za ta ƙaddamar da sabon tsarin makaman ta masu linzami masu iya ƙetare Nahiyoyi, wato Intercontinental Ballistic Missiles (ICBM), waɗanda ke da nisan kai har zuwa kilomita dubu 10,000.
Wannan nisan zai ba da damar kai farmaki ko isa kusan dukkanin ƙasashen Turai, wasu sassan Arewacin Amurka, har ma da ƙasar Amurka kanta.Masana harkar tsaro na duniya sun bayyana wannan mataki a matsayin sabon babi mai tayar da hankali a tarihi, wanda zai iya sake fasalin daidaiton ƙarfi tsakanin manyan ƙasashe
Kasar Iran dai ta zamanto wacce ta bayyana kaɗan daga ƙarfin makamanta a yaƙin kwanaki 12 da Haramtacciyar ƙasar Isra’ila ta tsokane ta hanyar kashe mata wasu daga cikin kwamandojinta
