Daga Masih Safiydul-Ali Allawee
Gwagwarmayar Tabbatar da Al-kur’ani a matsayin littafin hukunci a doron kasa, wanda shi ne aikin da Manzon Rahma (SAWA) ya kammala a Madina, shi ne ainihin bayyana soyayya da koyi da Manzon (SAWA).
Wakilin ‘Yan Uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), na garin Zaria, Sheikh Abdulhamid Bello ne ya bayyana hakan jiya a cikin jawabin Mauludin Manzo Allah (SAWA) wanda direbobi da kanikawan Zaria mabiya Sheikh Zakzakyn suka shirya a tashan ‘yan karfe na Sabon Garin Zaria.

Malamin wanda yayi dogon bayani akan Gwagwarmayar da Manzo Allah (SAWA) ya sha a Darul kufur a Makkah, wanda har ta kai ga kafiran Makkah suka azabtar da shi da kusan duk wadanda suka yi Imani da shi, irin su Bilal, ya jaddada cewa, amma, suka daure, har lokacin da aka yi hijrah zuwa Madina, lokacin ne suka samu sauki, domin a lokacin Musulunci ya sami daukaka.

Sheikh Bello ya kara da cewa da’awar komawa ga Allah ya gaji jarrabawa na gallazawa, amma idan an jure akan samu sassauci idan nasara ta zo.
Tun farko, kafin gabatar da jawabin nasa, Manyan Malamai irin su Malam Aliyu Iliyasu Ardido, da Sheikh Sanusi Khalifa, da Limamin Kwangila, Malam Iliyasu Imam, sun yi gwalagwalen bayanai akan wajibcin son Manzon Allah (SAWA) da hadin kan Musulmi.

Duka Malaman sun yi ittifaki akan hadin kan Musulmi shi ne nasarar su, kuma rarraba ita ce rushewar su, don haka suka bayyana alhininsu akan yadda wadansu da makiyya Manzo Allah suka samar a matsayin Malamai wadanda basu da aikin yi illa cin zarafin Shugaba kuma fiyayyen halitta (SAWA).

Kafin bayanin nasu, sai da daliban makarantun Fudiyoyi daban-daban suka gabatar da faretin jaddada wilaya da soyayya ga Manzo Allah (SAWA).
