Daga Zainab Ahmad
Hotunan shugaban Amurka Donald Trump, da suka nuna shi kamar yana bacci yayin wani taron gwamnati a ofishin White House (fadar shugaban kasa), sun tayar da ce-ce-ku-ce da martani da dama a shafukan sada zumunta, abin da ya sa aka nemi Fadar White House ta bayyana matsayinta.
Masu suka sun fassara hotunan da suka yaɗu a intanet a matsayin alamar gajiya da rashin mayar da hankali, duk da cewa gwamnatin Amurka ta dage cewa “shugaban yana cikin cikakken shiri da kuzari.”An ga Trump, mai shekara 79, a cikin hotunan taron da aka gudanar a ranar Alhamis, inda yake sanar da sabuwar mataki don rage farashin magungunan cutar ƙiba, tare da wasu jami’an gwamnati.A yayin taron, Trump ya rufe idonsa na ɗan lokaci, ko dai yana bacci ko yana ƙoƙarin buɗe idonsa da ƙyar, sannan kuma ana ganinsa yana shafar fuskarsa lokaci zuwa lokaci.
Gavin Newsom, gwamnan jihar California, ya yi tsokaci a shafin X (tsohon Twitter) yana cewa:“Trump mai bacci ya dawo,”yana nufin Yarfen da Trump ya yi ga tsohon shugaban ƙasa Joe Biden a baya da laƙabin “mai bacci.” ne ya dawo kan sa.
Me White House ta ce?
Mai magana da yawun White House, Taylor Rogers, ta ƙaryata cewa shugaban ya yi bacci a lokacin taron. Ta ce: “Shugaba Trump ya yi jawabi da cikakken bayani, ya amsa tambayoyin ’yan jarida, a yayin wani taron da ke nuna nasarar tarihi da za ta sa farashin magunguna masu muhimmanci ya ragu ga miliyoyin Amurkawa.”
Masu karatu mi za ku ce?
