Daga Aliyu Nasir
An samu rahotannin cewa rikici mai tsanani ya barke tsakanin ƙungiyar Boko Haram da ISWAP (Islamic State West Africa Province) a dajin Sambisa da kuma wasu yankuna kusa da Tafkin Chadi, lamarin da ya janyo rasa rayukan mayaƙa kusan 200 daga bangarorin biyu.
Majiyoyi daga jami’an tsaro da mazauna yankin sun tabbatar da cewa fafatawar ta fara ne bayan ISWAP ta kaddamar da farmaki kan wani sansanin Boko Haram a dajin Sambisa, inda suka yi amfani da manyan bindigogi, bama-bamai, da motocin yaki masu sulke.
Wani jami’in tsaro da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa:
“Yaƙin ya ɗauki awanni da dama. ISWAP ta fara farmaki ne domin karɓe sansanin. Mayaƙa da dama sun mutu, wasu kuma sun gudu cikin daji.”
A cewar majiyoyin, rikicin ya samo asali ne daga takun-saka kan ikon mallakar wasu yankuna masu mahimmanci da ke ba da damar samun kayan abinci, makamai, da kuma kuɗaɗe daga harajin da ake karɓa daga manoma da masu kamun kifi a yankin Tafkin Chadi.
Tun bayan mutuwar Abubakar Shekau a shekarar 2021, ISWAP ta ƙara samun ƙarfi wajen karɓe yankunan da Boko Haram ke iko da su, lamarin da ya haifar da gasa da gaba tsakanin kungiyoyin biyu.
A halin yanzu, ba a tabbatar da adadin wadanda suka ji rauni ba, amma masu sharhi na tsaro sun bayyana cewa wannan rikici yana iya sauya yanayin karfin kungiyoyin a yankin Arewa maso Gabas.
Jami’an tsaro sun ce za su ci gaba da sa ido yayin da sojojin Najeriya ke ƙoƙarin amfani da wannan rikici don ƙarfafa farmakinsu a kan dukkan kungiyoyin.
