Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta rasa Farfesa Sandra Ladi Adamu daga sashen Harkokin Yaɗa Labarai na jami’ar.Farfesa Sandra Ladi Adamu, wadda ta shahara kuma ta kasance Farfesa mace ta farko a fannin Jaridar Watsa Labarai (Broadcast Journalism) a Najeriya, ta rasu da safiyar yau a Asibitin Ƙasa da ke Abuja bayan ta yi fama da doguwar rashin lafiya.
An haifi Farfesa Ladi Adamu a ranar 17 ga Yuli, 1958, a Yaba, Legas.Mahaifinta, Adamu Pankshin, ya rasu ne yana hidimar ƙasa a matsayin soja tun tana ƙarama. Marigayi Adamu Pankshin, wanda aka fi sani da Sgt Major Adamu Pankshin, ya kafa tarihi a matsayin mutumin farko ɗan Najeriya da ya zama Regimental Sergeant Major (RSM) na rundunar injiniyoyin sojojin Najeriya da ke Kaduna.Ta yi karatu a Queen Amina College, Kakuri, Kaduna. Daga nan ta tafi Amurka inda ta samu digiri na farko (B.A.) a fannin Harkokin Yaɗa Labarai (Mass Communication) tare da ƙwarewa a rediyo da talabijin a Columbia College, Los Angeles, California (USA). Haka kuma ta yi karatu a City University, London, inda aka tura maki nata zuwa Columbia College, Los Angeles.
Ƙwazon neman ilimi ya sa Farfesa Ladi ta samu digirin M.A. a fannin Communication Arts (Film) daga Loyola Marymount University, Los Angeles, California (USA).Bayan haka, ta ƙara samun PGD a fannin Development Studies daga Mount Carmel Golda Meir Institute, Haifa (Israel), sannan daga baya ta kammala digirin digirgir (Ph.D.).
Farfesa Ladi Adamu ta fara aikinta a matsayin Public Relations Officer (PRO) a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Atlanta, Georgia, USA daga 1982 zuwa 1984.Daga nan ta koma Najeriya inda ta yi aiki a matsayin News Editor a NYSC, NTA Jos daga 1984 zuwa 1985, sannan daga 1985 zuwa 1987 ta ci gaba da aiki a NTA Jos.Daga bisani, Farfesa Ladi Adamu ta sami aiki a matsayin malamar jami’a a sashen Harkokin Yaɗa Labarai na Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, a shekarar 1999, inda ta ci gaba da aiki har ta zama Farfesa ta farko a fannin watsa labarai a Arewacin Najeriya.Ta bar bayan ta ‘ya’ya biyu waɗanda ke zaune a Abuja.
Allah Ya jikanta da rahama, ya kuma ba iyalanta da jami’ar ABU haƙuri da juriyar rashin ta.
