Yallaɓai! fatan kana lafiya, ya iyali, ayyuka da jama’a kuma?
Yallaɓai! ina cikin mutane bakwai na farko da suka san kai za a bai wa Shugabancin ƙaramar Hukumar Roni, hakan ya sa na ga dacewar turo maka wannan wasiƙa a daidai wannan tataɓurzar.
Yallaɓai! Na san kai mutumin kirki ne tun kafin ka zamanto Chairman kana da gidauniyar da kake tallafawa al’umma, don haka zamantowarka Chairman ƙara maka azama kawai ya yi.
Yallaɓai! sukar Shugabancin shugaba (duk yadda ya kai ga kyautatawa al’ummarsa kuwa) wannan ɗabi’ar mutane ce tun tale-talen shekaru ake aiwatar da shi, kama Abba Mu’azu Abiyos lallai zai ƙara maka tulin maƙiya ne kawai, a yayin da tauraronka (a fannin siyasa) mai haske zai dusashe a nan gaba, domin kuwa lallai a zagaye da kai akwai fuskokin waɗanda kan su kawai suke ka sani ba ci gaban al’umma ba, haka suka zagaye shugabannin da aka yi kafin ka, yanzu kuma sun watse sun zo gare ka, gobe kana sauka za ka nemi su ka rasa.Yallaɓai na san ka yi ayyuka masu yawa a Roni wanda kafin ka ba a yi irinsu ba, kamar yadda ka ke muhimmantar da ilimi ta hanyar biyawa Ɗalibai wajen ɗari bakwai kuɗin registration, gina roundabout a Roni, gina babban ɗakin taro, sayawa Ɗalibai Komfutoci ire-iren waɗannan ayyukan su ne na tallatawa a Duniya, amma bai wa masu sana’ar sayar da ruwa Kurarraki, ba a abun tallatawa ba ne ba, domin jama’a ba za su fahimci da kyakkyawar niyya ka yi ba, duk hakan abune mai kyau, amma cikin ayyukanka akwai waɗanda suka fi wannan kyau wanda ko a ƙasar waje aka gani ba wanda zai soki hakan domin kuwa ayyukan sun aikatu.
Yallaɓai! Tarihi ya rubuta cewa,an tsare masu faɗar ra’ayinsu a kan gwamnatin irinsu; Alexei Navalny Rasha 2012–2023, Maria Ressa Philippines 2019–2022,Liu Xiaobo,1989–2017,Ai Weiwei China 2011–2015, Ken Saro-Wiwa Najeriya 1995,Wole Soyinka 1967–1969, Václav Havel Czech Republic Marubuci da rajin dimokuraɗiyya 1979–1989,Loujain al-Hathloul Saudi Arabia 2018–2019,Andrei Sakharov USSR 1980–1986, Anna Politkovskaya Russia Jarida masu sukar Putin 2001–2006, Hrant Dink 2007 tsarewar ta mayar da waɗannan gwaraza a idon Duniya,a yayin da shugabannin da suka tsare su ake kallonsu a matsayin waɗanda suka take ‘yancin faɗar albarkacin baki. Ina cikin masoyanka da ba su ji daɗin tsare Abba Mu’azu Abiyos da ta bayyana kana da hannu a ciki ba kamar yadda abokinsa ya fallasa a ranar da aka kama Abiyos ɗin a shafinsa na Facebook.
Yallaɓai! Sunanka dole zai dawwama a cikin kundin tarihin Shugabanni waɗanda suka ciyar da Roni gaba (ko an so ko an ƙi), amma tsare irinsu matashi Abba Mu’azu Abiyos bai da ce da kai ba, domin kuwa ya kamata ne a ce lokaci bayan lokaci da kan ka kana leƙawa shafin Abiyos domin ganin wace sabuwar suka ya yi domin ka gyara, domin a cikin rubutun mai suka akwai gaskiyar da mai yabo ya danne da ba zai iya rubuta ko haskawa Shugaba ba.
Yallaɓai! na zaɓi rubuto maka wannan wasiƙar domin na san za ta riske ka. Ka huta lafiya.
Yusuf Kabiru shi ne Editan Jaridar MADUBI da kamfanin Abuja City Times Abuja ke wallafawa.Ya zo na biyu a gasar rubutu ta duniya da aka gudanar a ƙasar Iran a 2023.Ya rubuta a ƙalla muƙaloli 180 da aka wallafa a Jaridun ciki da wajen Nijeriya. Za a iya samunsa a kabiruyusuf533@gmail.com
