Hukumar Kula da Makaman Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta amince da wani kudiri da ke neman Iran ta ba da cikakken damar shiga wuraren nukiliyarta domin gudanar da bincike.
Sai dai gwamnatin Tehran ta yi watsi da kudirin, tana mai cewa matakin ba shi da adalci kuma yana sabawa yarjejeniyar da ake da ita tsakanin bangarorin biyu.
